Home Labarai Ya kamata a riƙa hukunci kan rashin biyan yan jarida albashi — NLC

Ya kamata a riƙa hukunci kan rashin biyan yan jarida albashi — NLC

0
Ya kamata a riƙa hukunci kan rashin biyan yan jarida albashi — NLC

Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, Joe Ajaero, ya yi kira da a rika hukunta gidajen jaridun da ba sa biyan ma’aikata albashi.

Ajaero ya kuma yi kira da a inganta albashi, inshora da kuma fansho ga ‘yan jarida a fadin kasar.

Ajaero ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ziyarci shugaban kungiyar Ƴan jarida ta Ƙasa, NUJ, Dakta Chris Isiguzo a Abuja.

Ya bayyana cewa yayin da ƴan jarida suka taka rawar gani wajen fafutukar kwato ƴancin kai da dimokuradiyyar da ƴan Nijeriya ke ciki a halin yanzu, abin takaici shi ne irin wadannan mutane sune ke rokon a rika basu albashi.

Shugaban kungiyar kwadagon ya ce aikin jarida na kara tabarbarewa a kowace rana, duk da cewa fasahar ta kara habaka aikin.

Ya kara da cewa, “Ina bayar da shawarar samar da wani dandali na tuntubar kafafen yada labarai duk bayan shekaru biyu don fitar da matsaya kan mafi ƙarancin albashi ga ‘yan jarida.

“Har ila yau, ya kamata a samu fensho da ya kamata dukkan ‘yan jarida su ji dadinsu bayan sun yi ritaya daga aiki. Inshora wani abu ne da ya kamata ƴan jarida su ji daɗin sa don su yi aiki sosai.”

Shugaban kwadagon ya jaddada cewa bai kamata a karfafa rashin biyan albashin ‘yan jarida ba kuma a dauke shi a matsayin “laifi”