
Wata ƙungiya mai rajin yaƙi da matsalar ƙwacen waya a Jihar Kano ta buƙaci gwamnati da majalisar dokokin jahar da su ayyana masu ƙwacen waya amatsayin ƴan fashi da makami.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci da a zartar musu da hukunci dai-dai da ƴan fashi da makami, kamar yanda doka ta tanada a tsarin dokokin jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Shugaban kungiyar, Abdulwahab Sa’id Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wata takarar bayan taro da kakakin ƙungiyar, Aminu Abba Kwaru ya sanyawa hannu a yau Talata a Kano.
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta umarci Hukumar Tace Finafinai ta jahar da ta hana masu shirya fina inan Hausa shirya fim masu nuna yanda ake ta’addanchi da gurɓata tarbiya, inda ta nuna cew irin waɗannan finafinan na taka muhimmiyar rawa wajan gurɓata tarbiyar matasa da kuma nuna dabarun ƙwacen waya da sauran laifuka.
A wani bangaren kuma kungiyar tayi kira ga majalisar malamai da limamai ta jahar Kano da su yi amfani da huɗubobin Juma’a wajen ci gaba da wayarwa da jama’a kai a kan hakkin baiwa yara tarbiya a Musulunci da kuma hukunchin da ubangiji Ya tanada ga duk uban da ya bada gudunmawa wajan lalacewar tarbiyar ƴaƴansa.
3. Shugaban kuma yayi kira ga masarautar jahar kano data umarci hakimai, dagatai da masu unguwanni da lallai su samar da kwamitin tsaro a cikin dukkan unguwannin jahar domin taimakawa jamian tsaro da bayanan sirri.