
A jiya Laraba ne dai Kamfanin Ɗangote ya ƙaddamar da wani shiri na horas da ƴan jarida 60 daga jihohin arewa-maso-yamma a Jihar Kano.
A cewar fannin hulɗar jama’a na kafanin, horon wani ɓangare ne na tsarin aiyukan sauke nauyin al’umma da kamfanin ke yi.
Horon, a cewar kamfanin, an yi shi ne da nufin ƙara ƙaimi kan fasahar kafafen yaɗa labarai, wan da aka gaiyato ƴan jarida daga jihohin Sokoto, Katsina, Kebbi, Kano, Kaduna, da kuma Jigawa
Horon na haɗin gwiwa ne da Kamfanin Folio Media and Creative Academy, inda kamfanin ya ce an gudanar da shi a baya a wasu shiyyoyin ƙasar.
Taron na kwanaki uku an yi masa take da “Haɗewar aikin jarida ta hanyar fasaha”
A taron da aka fara gudanar da horon a Kano ranar Laraba, shugaban rukunin kamfanin, Branding and Communication, Anthony Chiejina, ya ce an shirya horon ne domin inganta kwazon ‘yan jarida kan dabarun yada labarai.
Ya ce horon zai taimaka wajen samar wa manema labarai damar tunkarar kalubalen da ke tattare da sauya salo daga gargajiya zuwa sabbin dabarun yada labarai.
Ya bayyana cewa akwai alaka mai kyau tsakanin kamfanin da kafafen yada Labarai.
Mai kula da wannan shiri a Folio Media and Creative Academy, Alabi Pius, ya ce cihiyar (FMCA) ita ce ta horar da Folio Communications Plc.
Mawallafin na jaridar Daily Times, ya kara da cewa an shirya wannan horon ne domin baiwa ‘yan jarida da shugabannin kafafen yada labarai da jami’an hulda da jama’a damana wasu fannoni daban
A nasa jawabin, wani malami a Jami’ar Bayero Kano, Dokta Mukhtari Magaji, ya bukaci ‘yan jarida da su yi shirin sauyawa zuwa zamani, domin fasahar za ta kara musu karfin gwiwa da kuma sanya su cikin sabuwar duniya.
Dokta Magaji ya bayyana cewa hada aikin yada labarai na nufin amfani da rubutu, sauti, da bidiyo ta hanyar sadarwa guda ɗaya.
Sauran malaman da za su yi jawabi a shirin horaswar sun hada da Dr. Bala Muhammad, tsohon dan jarida a kafar yada labarai ta BBC da ke Landan kuma malami a Jami’ar Bayero Kano; da kuma Dr. Saminu Umar, shima malami a wannan jami’ar.
A nasa jawabin, wani da ya halarci taron kuma wanda ya samar da shafin intanet na “Good Governanc”, Dakta Aliyu Machika, ya ce horon ya yi daidai da lokaci domin zai baiwa manema labarai a shiyyar Arewa maso Yamma damar kara kaimi da kuma kara musu karfin tattalin arziki.