
Abdu Mohammed, Manajan Darakta na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos, JED, ya tabbatar da ɗaukar ma’aikata 121 da suka kwashe sama da shekaru biyu suna aiki a kamfanin.
Mohammed ya sanar da hakan ne a wata ganawa da ya yi da ma’aikatan yankin Jos Metro, Gangere.
Friday Iliya, shugaban sashen sadarwa na kamfanin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi a Jos.
Manajan daraktan, wanda ya fara aiki a mako guda da ya wuce, ya shawarci ma’aikatan da su yi iya kokarinsu wajen samun nasarar kamfanin da samar da hidima mai inganci.
“Muna kuma aiki kan ƙarin matsayi na ku wanda a ka ɗauki tsawon lokaci ba a aiwatar ba.
“Hanya daya tilo da za mu iya cimma hakan cikin hanzari ita ce yin aiki don sake farfado da arzikin kamfanin a halin yanzu.
“Dole ne ku canza hanyar bunƙasa tattalin arzikin kamfanin nan; za mu baiwa dukkan ku aiki da kuma sanya ido a kan ƙwazon ku sannan za mu riƙa baku taimako wajen yin aikinku, ”in ji shi.
Mohammed ya kuma bukaci ma’aikatan da su tabbatar da cewa kwastomomi sun samu tagomashin kuɗin da su ke biya ta hanyar jin dadin samar da wutar lantarki mai inganci da na yau da kullum a matsayin wani abin da zai gamsar da abokan ciniki.