Home Kasuwanci Kamfanin simintin Dangote ya samu naira biliyan N413.2 kuɗaɗen shiga a watanni 3

Kamfanin simintin Dangote ya samu naira biliyan N413.2 kuɗaɗen shiga a watanni 3

0
Kamfanin simintin Dangote ya samu naira biliyan N413.2 kuɗaɗen shiga a watanni 3

 

Kamfanin simintin Dangote ya samu ƙaruwar kashi 24.2 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar kuɗi ta 2022 kuma ya samu ƙaruwar kashi 18 cikin 100 na ribar da yake samu bayan haraji a dai wannan lokacin.

A wani rahoto da ba a ƙididdige ba na tsawon watanni uku, wanda ya kare a ranar 31 ga Maris 2022, ya nuna kuɗaɗen shiga na Naira biliyan 413.2 da kuma riba bayan haraji ts Naira biliyan 105.9.

Binciken sakamakon da kamfanin simintin ya yi na watanni uku ya nuna cewa Dangote ya sayar da jimillar siminti tan miliyan 7.2, inda a Najeriya kaɗai ya sayar da tan miliyan 4.8 yayin da sauran kasashen Afirka suka cikashe miliyan 2.4.

Babban jami’in kamfanin Dangote Cement, Michel Puchercos, ya bayyana cewa kamfanin ya fara rubu’in farko bisa kyakkyawan yanayi duk da sabbin rashin tabbas da yanayin duniya ke kawowa.

Ya ce ƙaruwar da aka samu a cikin kuɗaɗen shiga da kuma samun riba ya haifar da haɓɓakar samun kudade mai a rukunin kamfanin.

A cewarsa, ribar da aka samu bayan Haraji ta tashi zuwa Naira biliyan 105.9, wanda ya karu da kashi 18 idan aka kwatanta da bara, yayin da rukunin EBITDA ya tashi zuwa Naira biliyan 211.0, da kashi 18.6 bisa 100 da EBITDA da kashi 51.1 cikin dari.