
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun ƙasa na Jihar Oyo, Abiodun Oni, ya ce aƙalla kamfanonin kwasar shara 197 ne su ka sake neman kwangilar a karkashin tsarin masana’antu masu zaman kansu, PSP.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido na jihar, Dr Wasiu Olatunbosun ya fitar ranar Litinin a Ibadan.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin jihar ta soke kwangilar da ta baiwa Kamfanonin saboda rashin ingantaccen aikin kwashe sahara.
Sakamakon haka gwamnati ta naɗa wani kamfani mai suna Mottanai Recycling a matsayin mai ba da shawara kan harkokin sharar gida a jihar, a matsayin wani mataki na samar da sauyi a fannin muhalli.
A cewar sanarwar, Mista Oni ya tabbatar da kudurin gwamnati na tabbatar da cewa ƴan kasar su kasance cikin tsafta da muhalli.
Sai dai kuma Kwamishinan ya fayyace cewa sake neman kwangilar da kamfanonin za su yi ba ya na nufin tabbacin samu ba ne.