
Hassan Y.A Malik
Wani rahoto da asusun kula da kananan yara na gaggawa, UNICEF ya fitar a yau Talata, ya bayyana cewa akalla yara kanana mata (wadanda ba su cika shekarun aure ba) miliyan 12 a ke aurarwa a fadin duniya a kowace shekara.
Wannan sabon rahoto ya nuna faduwa a adadin da kaso 15 cikin a shekaru goma da suka wuce, daga yarinya 1 a kowane yara mata 4 zuwa yarinya 1 a kowane yara mata 5 da ake aurarwa a duniya.
UNICEF ta yi gargadin cewa in har aka ci gaba da tafiya a haka, to, kafin shekarar 2030 za a kai yanayin da yara mata kanana miliyan 150 ne za su fuskanci aure kafin shekarunsu na haihuwa ya kai 18.
“Da zarar an tilasta yarinya ta yi aure kafin ta cika shekarun mallakar hankali da iya daukar dawainiyar aure, to, fa, hakan zai tasirantu a rayuwarta tasiri maras kyau na har abada.”
“Yiwuwar kammala karatunta da samun ilimi mai inganci zai zama kila-wa-kala, haka kuma yiwuwar fuskantar barazanar cin zarafi daga mijinta da kuma fuskantar hatsari a lokacin rainon ciki da haihuwa zai girmama,” inji Anju Malhotra, wacce ita ce mashawarciyar hukumar UNICEF kan harkokin jinsi.
A yankin Asiya ta kudu, an samu raguwar adadin aurar da kananan yara mata daga kaso 50 zuwa kaso 30 cikin 100.
A yankin Afirka da ke da makwabtaka da sahara kuwa, an samu raguwar aurar da kananan yara ne daga kaso 43 a shekaru 10 da suka wuce zuwa kaso 38 a a yanzu.
Bincike ya gwada cewa a kalla mata da adadinsu ya kai miliyan 650 a fadin duniya an musu aure ne kafin su cika shekaru 18 da haihuwa.
Majalisar dinkin duniya na son kawo karshen auren kananan yara ne a shekarar 2030.