
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci bikin rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sabon mataimakin Gwamnan Kano wanda majalisar dokokin jihar ta gama tantancewa a ranar Talata.
Nasiru Gawuna ya zama sabon mataimakin Gwamnan Kano tun bayan da tsohon mataimakin Gwamna Hafizu Abubakar yayi murabus daga mukamin.