Home Labarai KANO: Kwankwasiyya da Gandujiyya na barazana ga zaman lafiyar al’umma

KANO: Kwankwasiyya da Gandujiyya na barazana ga zaman lafiyar al’umma

0
KANO: Kwankwasiyya da Gandujiyya na barazana ga zaman lafiyar al’umma
Sanata Kwankwaso daga hagu, sai Gwamna Ganduje daga dama

Wata fitacciyar kungiyar taimakon al’umma da cigabansu a jihar Kano mai suna CITAD ta bayyana rashin gamsuwa bisa yada rikicin Kwankwasiyya da Gandujiyya a jihar ke naman jefa rayuwar al’umma cikin garari da rudani.

Babbab jami’in gudanarwa na kungiyar, Isah Garba, shi ne ya bayyana hakan ga manema abarai a Kano a wani taron ‘yan jarida da kungiyar ta kirawo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewar, bayan cewar ‘yan Gandujiyya na goyon bayan Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje, a daya bangaren kuma, ‘yan Kwankwasiyya na goyon bayan tsohon Gwamnan Rabiu Kwankwaso.

Batun wannan sabatta juyatta da ake yi a tsakanin kungiyoyin siyasar biyu na kara sanya shakku game da lamuran siyasa a jihar Kano kasancewarta cibiya ta Siyasa a Arewacin Najeriya, haka kuma barazanar zaman lafiyar da ake da ita a jihar na kara bayyana a dalilin wannan rikicin a jihar.

“Yanayin siyasar jihar Kano a ‘yan kwanakinnan ya zama wani abin tattaunawa sosai game da samun zaman lafiyar jihar”

“Cigaba da samun sabanin da ake yi tsakanin bangaren Kwankwasiyya da na Gandujiyya a karkashin jam’iyyar APC na kara nuna yadda kurar yakin siyaye ke kara turnukewa a kullum”

“Wannan kuma barana ce mai girma dan gane da tsaron lafiya da kuma dukiyar al’umma, a Kanon da ake ganin ita ce cibiyar Kasuwanci ta Najeriya, haka kuma na kara yadda bangaren siyasa na Arewa yake daukar wani mawuyacin yanayi” A cewarsa.

Yace a yanzu abubuwa sun dauki zafi dangane da yadda ake kara yamutsa gashin baki tsakanin bangarorin siyasar guda biyu, musamman akan shirin ziyarar da tsohon Gwamnan kuma Sanata jagoron bangaren Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso yake shirin kawowa a karshen watannan.

Ya buga misali da kalaman baya bayannan da aka jiyo Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman Abdullahi Abbas Sunusi aka jiyo shi yanayi, inda yake kiran magoya bayansu da su yiwa tsohon gwamnan jifan Shedan idan ya zo Kano.

“A matsayin kungiyarmu na masu son wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, muna da damuwa kwarai da gaske kan abinda yake faruwa”

Daga nan yayi kira ga dukkan bangarorin siyasar guda biyu da su baiwa Shedan kunya wajen marawa batun zaman liya a jihar baya, domin bunkasar arziki da cigaban al’ummar kano da ma kasa baaki daya.

Haka kuma, yayi kira ga dukkan bangarorin jam’an tsaro da su sanya ido sosai tare da bincikar dukkan wani abu da ka iya hautsina al’umma ta fuskar zaman lafiya akan wannan ziyara da tsohon Gwamnan zai kawo jihar Kano.

NAN