Home Lafiya Kano: Mata ta haihu yayin taron bita kan lafiyar mata a asibiti

Kano: Mata ta haihu yayin taron bita kan lafiyar mata a asibiti

0
Kano: Mata ta haihu yayin taron bita kan lafiyar mata a asibiti

 

 

Wata maya mai shekaru 30, Hadiza Ayuba ta haihu yayin wani taron wayar da kai da asibitin koyarwa na Aminu Kano, tare da haɗin gwiwar ɗan Majalisar Tarayya, mai wakiltar mazabar Dawakin Kudu da Warawa, Alhaji Mustapha Bala Dawakin su ka shirya.

Matar, mai ƴaƴa takwas ta kamu da naƙuda ne jim kaɗan bayan jami’an lafiya na asibitin koyarwa na Aminu kano sun fara wayar da kan mata kan mahimmancin kula da haihuwa da rigakafi da kuma yadda ake gano matsalolin da ke da alaƙa da juna biyu.

Da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan ta haifi ‘ya mace tare da taimakon ma’aikatan sashen haihuwa na asibitin Aminu Kano, Hadiza ta yabawa wadanda suka shirya taron, inda ta ce har abada za ta ci gaba da godiya ga wadanda suka taimaka mata da kuma kayan haihuwa da aka ba su.

Tun da farko a nata jawabin, Jami’ar kiwon lafiya Nafisa Zubairu, ta umarci mata masu juna biyu da su ziyarci asibitoci domin kula da lafiyar haihuwa.

Ta bayyana zubar jini da amai da ciwon kai da zazzabi da ciwon ciki a matsayin wasu abubuwan da ke haifar da mace-macen mata masu juna biyu.