
Rundunar ƴan sanda a jihar Kano, ta ce an samu gawar wasu ma’aurata a kan gadon su na aure a mace a karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar, wadanda ake kyautata zaton sun mutu ne sakamakon shakewar hayakin gawayi.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ƴan sandan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Kano a jiya Laraba.
Ya bayyana sunayen ma’auratan da Sulaiman Idris, mai shekaru 28 da Maimuna Haliru ƴar shekara 20.
“Mun samu rahoto a ranar 3 ga watan Janairu da misalin karfe 9:00 na dare daga kauyen Ƙwa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa cewa an gano wasu ma’aurata, ba su fito waje ba ba tun daga ranar 2 ga watan Janairu da misalin karfe 11:00 na dare.
“Lokacin da kakar Idris ta ɓalle kofar, sai ta ga cewa ma’auratan na kwance a kan gado amma ba sa motsi ga kuma ƙaurin hayaki ya mamaye dakin.
“Bayan samun rahoton, kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda, ya umurci tawagar ƴan sanda karkashin jagorancin CSP Ahmed Hamza, DPO na Dawakin Tofa da su je wurin.
“Su na zuwa sai su ka kwashe gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su. Sai aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano inda likita ya tabbatar da mutuwarsu,” inji Haruna Kiyawa.
Koyawa ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa ma’auratan da su ka mutu sun kunna wutar gawayi don dumama dakin saboda sanyi.