
Shatu Garko, sananniyar mai kwalliyar hijabi, ta lashe gasar sarauniyar kyau ta bana.
Shatu, ƴar shekara 18 ta wakilci arewa-Maso-Yammacin Nijeriya a gasar.
Shatu, wacce ta yi shura wajen adon hijabi kuma mafi ƙarancin shekaru a cikin ƴan takarar, ta lashe gasar karo na 44 yayin da a ka bata lambar kyautar a Legas a jiya Juma’a da daddare.
Ta doke ƴan takara 17 ta zamto mace mai adon hijabi ta farko da ta lashe gasar sarauniyar kyau.