Home Siyasa Kano 2023: Zaura ya yi mubaya’a ga Gawuna, inda ya yanki fom ɗin takarar Sanata

Kano 2023: Zaura ya yi mubaya’a ga Gawuna, inda ya yanki fom ɗin takarar Sanata

0
Kano 2023: Zaura ya yi mubaya’a ga Gawuna, inda ya yanki fom ɗin takarar Sanata

 

Na gaba-gaba a takarar gwamna a Jihar Kano a jam’iyar APC, Abdussalam Abdulkarim Zaura ya yi mubaya’a ga Mataimakin Gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamna.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tuni dai Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya zaɓi Gawuna da tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo a matsayin ɗan takarar gwamna da mataimaki a zaɓe mai zuwa na 2023.

Sai dai kuma bayan wannan mataki ne, sai Zaura, wanda a ka fi sani da A. A. Zaura, ya ce ya janye takarar sa ga Gawuna, inda ya sayi fim ɗin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

A wata sanrwa da ya sanya wa hannu a ka kuma wallafa a shafin Facebook na yakin neman zaben sa, Zaura ya ce yana goyon bayan takarar ta Gawuna/Garo.

“Ina mai farin cikin sanar da magoya bayana da na al’umma baki ɗaya cewa, bayan doguwar tattaunawa domin a cimma matsaya ɗaya ta tsaida ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen fidda gwani dake zuwa nan da ƴan kwanaki a ƙarƙashin jagorancin jagoranmu His Excellency Dr Abdullahi Umar Ganduje an cimma matsaya kamara haka:-

” His Excellency, Dr. Nasir Yusuf Gawuna shine zai zama ɗan takaran mu na gwamna a wannan zaɓen fidda gwani, wanda bayan an kammala muke fata ya zama ɗan takarar Gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin inuwar jam’iyarmu ta APC a zaɓukan shekarar 2023.

“Hon. Murtala Sule Garo, tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masauratu zai zama ɗan takarar mataimakin gwamna.

” Ni Kuma zanyi takarar kujerar Sanata a shiyar Kano ta tsakiya da yaddar ALLAH.

“Inaso al’umma su sani cewa ban shigo siyasa dan a mutu ko ayi rai ba, kuma banzo siyasa don dole sai ni ba. Babban abinda ya kawoni shine domin ina ganin inada wata gudunmuwa da zan iya bayarwa ta musamman wadda zata kawowa al’umma sauƙi. Kuma a ƙarƙashin wannan tsari zanyi iya yina domin samun hakan insha ALLAH.

“Tabbas na yarda, da ni da jama’a ta za muyi iya yinmu don ganin samun nasarar tikitin Gawuna/Garo a dukkanin zaɓuɓɓuka masu zuwa,” in ji Zaura.