Home Rahoto na Musamman Kanwa: Garin da rashin ingantaccen ruwan sha ya hana yara zuwa makaranta a Jihar Kano

Kanwa: Garin da rashin ingantaccen ruwan sha ya hana yara zuwa makaranta a Jihar Kano

0
Kanwa: Garin da rashin ingantaccen ruwan sha ya hana yara zuwa makaranta a Jihar Kano
Abdullahi Muhammad, mai shekaru 52, mai sana’ar acaɓa ne, inda ya kan fita da wuri don samun na abinci. Yawanci yana fita da sassafe saboda lokacin ne fasinjoji ke gaggawar tafiya inda za su je.
A ko da yaushe kafin ya fita aiki da babur ɗinsa, Muhammad ya dinga ƙwala wa ƴaƴansa kira kenan domin su bi ayarin sauran yara don zuwa nemo ruwan amfani, wanda ya kamata ace wannan lokacin makaranta za su tafi.
Malam Muhammad, wanda ke zaune a unguwar Kanwa, Ƙaramar Hukumar Warawa a jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya, ya koka kan rashin samun ruwan sha ingantacce da kuma yanda rashin ruwa ya yi tasiri ga rayuwarsu. Mazauna yankin kan yi tafiya mai nisa don neman ruwa mai kyau.
“Rashin ruwa ya jawo mana wahalhalu masu matukar misaltuwa. Har yanzu gwamnati ba ta samar mana da ruwan famfo ba duk da kiran da muke yi na neman a taimaka mana a wannan fanni,” kamar yadda ya shaida wa Jaridar DAILY NIGERIAN, inda ya kara da kiran wasu ‘yan uwansa da su zo suma su labarta na su kalubalen.
Muhammad ya ce ’ya’yansa tun karfe 4 na safe suke farkawa daga bacci inda wani lokacin su ke yin tattaki mai nisan kilomita 20 zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su kamar Makoli da Zogarawa domin dibar ruwa a rijiyar burtsatse, inda ya ce idan ba haka ba, shi da iyalansa sai dai fa su yi amfani da ruwan rafin da suke da shi mai datti don sha da sauran amfanin gida.
Matsalar Samun ruwan sha ya zama ruwan dare gama gari a yankunan karkara a Najeriya. A cewar UNICEF, samun tsaftataccen ruwan sha ya kasance babban kalubale ga akasarin ‘yan Najeriya, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara. An yi kiyasin cewa kimanin mutane miliyan 69 ne ba sa samun ruwa mai tsafta sannan kuma mazauna karkara miliyan 19 suna tafiya mai nisa don dibar ruwa mara tsafta daga tabkuna, koguna da rafi.
“Yara ba sa zuwa makaranta” – Cewar Shugaban makarantar firamare ta Kanwa
 Rashin samun ruwa, musamman a yankunan karkara  alama ce ta wasu matsaloli da ke dankare a kasa.  Daya daga cikin wadannan nakasu sun hada da ilimin yara.Yaran Malam Muhammad sun dade da daina zuwa makaranta.
“‘Ya’yana hudu ba sa makaranta. Daya daga cikinsu ya shafe shekaru 2, daya kuma shekaru 4 zuwan ba zai yiwu ba saboda nauyin da ke kansu. Ba su da wani aiki sai debo ruwa, suna farawa daga karfe 4 na safe, wani lokaci sai yamma suke dawowa. Ina da iyalai kuma muna amfani da ruwa mai yawa a kullum.”
Ziyarar da muka kai makarantar firamare da ke garin Kanwa wanda ke kusa da unguwar Malam Muhammad ranar Juma’a, 10 ga watan Yuni, mun sami labari mai ban tsoro. Duk yawan ɗaliban makarantar aji daya kawai suke iya cikawa. Makarantar tana da ajujuwa hudu kawai.
A cewar shugaban makarantar, Sunusi Jafar, yaran ba ko yaushe suke zuwa makarant ba ,a kullum rashin zuwan dalibai karuwa yake yi.
Yawancin yaran wannan unguwar ba sa zuwa makaranta.  Shi ya sa za ka ga wasu azuzuwan babu kowa.  Da na tambayi wasu iyayen yaran, sai suka ce yaran suna taimaka musu wajen samo ruwa.
Wannan abin takaici ne,Yanzu zaka ga dalibi a cikin makarantar,gobe ba za ka kara ganin sa ba duk saboda ruwa.
 Duk da dokar kasa na ba da ilimin firamare kyauta, kimanin yara miliyan 10.5 ‘yan kimanin shekaru 5-14 ne ba sa zuwa makaranta, kamar yadda al’ummar yankin Kanwa suka daina zuwa makaranta. Sake dawo da yaran da ba su karatu zuwa makaranta abu ne da ke haifar da babban kalubale.
Kwararre a fannin ilimi a UNICEF, Mutaka Muktarthat, a cikin wata takarda da aka gabatar a wani taron tattaunawa a watan Agustan shekarar 2020 kan hanyoyi da za a abi don samar wa yara Almajira makoma, ya ce jihar Kano ce ta fi kowacce jiha a yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan.
Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, a cikin wani rahoto da aka fitar a shekarar 2020, ta bayyana cewa kashi daya bisa hudu na yaran Najeriya kimanin miliyan 40.8 da suka isa fara zuwa makaranta ba sa zuwa makarantar firamare. Jihohi 10 da ke kan gaba gaba a jadawali suna da kusan miliyan 5.2 a ciki yara miliyan 10.2 na ƙasar da ba sa zuwa makaranta. Jihar Kano ita ce ta daya da Kusan yara 989,234, sai Akwa-Ibom 581,800 Katsina 536,122 da Kaduna 524,670.
“Muna yawan kwanciya rashin lafiya saboda muna shan ruwan da dabbobin mu ke sha” – cewar mazaunin yankin.
Rashin samun Ingantacce ruwa yana haifar da illa ga lafiyar mazauna wannan yaki.  Salmanu Isah, mai shekaru 33, yana kiwon shanu inda kiwon sa na yau da kullun baya gaza yin tattaki sama da kilomita 20 daga Kanwa zuwa unguwar Zogarawa domin neman ruwa.Tare da shanunsa da jarkunansa da kuma daya daga cikin ‘ya’yansa, ya ce babu ranar da baya tafiya neman ruwa wa dabbobin sa da kuma kansa ba.
“Nakan damu a duk lokacin da na ga ‘ya’yana suna diban ruwa, ba sa zuwa makaranta kusan watanni 4, amma ba ni da yadda zan yi. Muna buƙatar ruwa mai tsabta ko mai datti. Saboda ruwan datti da muke sha, mun kamu da cututtuka Iri daban-daban musamman kwalara, da taifot,” inji Malam Isah.
Nura Yakubu, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa rashin tsaftataccen ruwan sha na daya daga cikin dalilan da suka sa al’ummar yankin ke fuskantar kuncin rayuwa. “Mun dade muna fuskantar matsalar ruwa. Babbar matsalar mu shine nisa. Muna biyan Naira 150 don hayan keke domin mu samu ruwa mai tsafta.  Ruwan da muke debowa shi muke sha,muke dafa abinci da alwala ” inji shi.
 Bayanai da aka fitar a cikin shekarar 2017 da ga Cibiyar Kula da Cututtuka, CDC, sun bayyana cewa maɓuɓɓugar ruwa mara tsafta, rashin samun damar yin amfani da kayan tsaftace hannu na yau da kullun, da rashin tsaftar muhalli suna da alaƙa da mutuwar mutane miliyan 1.5 a duk duniya kowace shekara.
A al’ummar Kanwa, al’umma ce da cutar kwalara ta yi katutu,  Ibrahim Zakariyyah, mai shekaru 53, ya shafe makonni yana shan hadin ganye daban-daban don magance cutar kwalara da ta yi kamari a wannan yankin.
“A yanzu haka da nake magana da ku, ba ni da ƙarfi sosai a jikina. Wannan cutar ta kwalara ta fara ne tun a shekarar 2020 kuma tun daga lokacin nake dafa ganye da sauran magungunan gargajiya.
Lokacin da na je asibiti a shekarar da ta gabata, sai suka ce min na kamu da cutar kwalara saboda ruwan datti da nake sha. Sun ba ni wasu takardun magani wanda dole na in sha.  Wani lokaci, nakan yi lafiya na tsawon mako guda ko fiye amma daga baya abin (rashin lafiya) sai ya sake tashi,” in ji Malam Zakariyyah.
 Kuma ana samun rahotannin yin garkuwa da mutane, da cin zarafin jama’a a duk lokacin da suka je neman ruwa.
 Sumayya Usmanu, mai shekara 21, ta bayyana wani da wani lamari da ya faru da ita kwanan nan. Ta yi tattaki zuwa makwabtan unguwa da ke kusa da su don neman ruwa ko da isar ta sai ta hau layi.  Sai da gari ya yi duhu sannan layi ya iso kanta ba yadda ta iya haka nan ta kama hanyar unguwarsu da daddare.
“Wasu mutane uku ne da ban san ko su waye ba suka yi yunkurin sace ni, na yi sa’a wasu mafarauta ne su ka yi nasarar kubutar da ni. Na ji rauni sosai a wannan lokaci inda na yanke shawara ba zan sa ke kaiwa dare ba in naje diban ruwa. Wannan Abu ya kasance mai matukar ban tsoro sosai,” in ji Sumayya Usmanu.
Sakamakon gwajin ruwa da akayi mai ban mamaki.
DAILY NIGERIAN  ta gabatar da ruwan da mazauna garin ke sha don gwaji inda aka kai shi dakin gwaje-gwaje. Gwajin da aka gudanar a MAMS Consultancy Services, Kano, wanda ya nuna cewa ruwan da al’umman ke sha ba shi da kyau, akwai kwayoyin cuta masu illa.
Dangane da sakamakon gwajin, an sami Psedomonas aeruginosa, daya daga cikin mafi hatsarin ƙwayoyin cuta da aka sani wanda yake haifar da zazzaɓi, amai da ciwon ciki ya kasance an same shi sosai a cikin ruwan.Sannan ruwan yana ƙunshe da adadi mai yawa na ƙwayoyin cuta coliform bacteria, da sauran su.Sannan akwai ƙwayoyin cuta masu cutarwa.
Wani rahoto na shekarar 2019  da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya da UNICEF ta fitar, ya nuna cewa kashi ɗaya bisa uku na al’ummar Najeriya na shan gurɓataccen ruwa yayin da yara 130,000 ke mutuwa a duk shekara sakamakon kamuwa da cututtuka da suka shafi ruwa.
Kwayoyin cutar Coliform sun haɗa da Escherichia coli, da nau’in Salmonella. Ida aka samu waɗannan nau’ikan kwayoyin cuta a cikin kowane ruwan sha sukan haifar da cututtuka masu haɗari kamar tyfot, gudawa da ciwon hanta da dai sauransu.
 
“Na budi ido da wahalar karancin ruwan sha” – Sabitu Hamza
Sabitu Hamza, shugaban mazauna Kanwa na zaune a kofar gidansa rike da magogi a bakinsa  jefi -jefi ya ya kan daga ido ya kalli mazauna garin da ke ta kaikawo wajen fafutukar tura amalanke mai cike da jarkokin ruwa.  An haifi shi a garin garin Kanwa wanda ya kasance shine dagacin wannan yankin dan kimanin shekaru 56 .Ya koka da cewa shi da jama’arsa har yanzu ba su fara morar gwamnati ba inda suke fama da karancin ruwa wanda tun yana karami ake fama da ita.
“Na girma na samu ana fama da wannan matsalar ruwa. Dattawanmu sun sha gaya mana cewa wannan zamani na rashin ruwa ya fi na lokacin su. Ko sanda na ke makarantar firamare sai na debo ruwa kafin na je makaranta wanda rashin yin hakan na iya haifar da matsalar rashin ruwa mai tsanani a gidan.Na tuna wasu shekaru da suka wuce zan fita da safe neman ruwa sai yamma zan koma gida,” inji shi.
Ya bayyana cewa rashin zuwa makaranta da kuma shiga makarantu yana daya daga cikin illar da rashin ruwan sha ya haifar a cikin al’umma.
 “Rashin tsaftar ruwan da muke sha shi ya ke haifar mana da cututtuka da dama amma ba mu da yadda za mu yi.Sau da yawa muna samun barkewar cututtuka, amma a ‘yan shekaru nan an samu sauki sosai.Gangar jikin mu yariga ya saba. ‘Ya’yanmu sun daina zuwa makaranta saboda wannan matsalar domin a kowace safiya sai sun debo ruwa” ya kara bayyanawa.
 Bugu da kari, Muhammad Khalid, mai shekaru 35, ya kasance yana jan amalanken ruwa mai dauke a jarkoki goma sha biyar. Ya goge zufan da ke goshin sa, tare da matsawa kusa da rafin da suke diban ruwa a ko yaushe.
 “Tun da garin Allah ya waye diban ruwa nake yi wanan shine sawuna na biyu. Duk lokacin da nake son yarana su tafi makaranta, sai dai na fito da sassafe don dibar ruwa amma hakan yana nuna cewa ba zan samu kudin shiga ba a wannan rana,” in ji Malam Khalid, in da yake nuna yaransa.
Ya kara da cewa duk lokacin da bai debo ruwa ba, to fa yaransa ba za su tafi makaranta ba,su za su je neman ruwa.
 “A kullum, iyalina na amfani da matsakaicin Jarkan ruwa guda 8” in ji shi yayin da yake korafin tsadar sayen ruwan rijiyoyin burtsatse a yankin.
“Suna sayar da jarka mai cin lita 25 akan Naira 25 zuwa Naira 30. Da kyar muke iya siya. A duk lokacin da banida kudi ba ni da wani zabi illa mu yi amfani da ruwan rafin mu mara tsafta” inji shi.
Biliyoyin Nairori da aka zuba a harkar ruwan Kano har yanzu ba a samu yadda ake so ba.
 A shekarar 2018, Hukumar Bunkasa Cigaban Kasar Faransa, AFD, ta tallafa wa aikin ruwan Kano da kudi Naira biliyan 28.45 (€64.75 miliyan), amma har yanzu al’ummomin jihar sun kasa samun tsaftataccen ruwan sha.
 A ranar 14 ga watan Agusta, shekarar 2018, Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya ta hannun mai girma Minista, Suleiman Adamu, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa na fadada samar da ruwa, tsaftar muhalli PEWASH, da hadin gwiwan gwamnatin jihar Kano.
A yayin taron, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana jin dadinsa kan wannan yarjejeniyar, inda ya kara da cewa Naira biliyan 12.7 da aka ware domin gudanar da aikin zai taimaka matuka wajen inganta samar da ruwan sha a yankunan karkarar jihar.
“Jimillar haɗin gwiwar yana cikin yanki Naira biliyan 12.7 wanda kuɗi ne mai tarin yawa, wanda hakan ya nuna irin yaddada maigirma shugaban ƙasa ya damu da talakawan karkara waɗanda galibi suka dogara da fanfunan,da rijiyoyin burtsatse.”  yace.
 A watan Oktoban shekarar 2021, gwamnatin jihar Kano ta kuma amince da kashe Naira biliyan 137 domin samar da ruwan sha domin ganin an yi yaki da cutar kwalara da sauran kalubale. A bana Hukumar Raya Kasa da Kasa ta Amurka, USAID, ta hannun abokan huldar ci gaba, ta kaddamar da shirin inganta ruwa da tsaftar muhalli na dala miliyan 3.5 na tsawon shekaru uku, domin inganta tsaftar ruwa a jihohin Jigawa da Kano.
Abin mamaki, duk da kasancewar garin Kanwa ba bu ruwa, ba taba amfana da duk wani aikin samar da ruwan sha na karkara da akeyi a jihar ba. Aikin rijiyar burtsatse da aka yi a garin don magance matsalar karancin ruwa abin bai dade ba ya watse. A cewar wani mazaunin unguwar, Suaibu Musa, an gudanar da aikin ne shekaru kadan da suka gabata a karkashin shirin gwamnatin tarayya na shiyyar.
Malam Musa ya shaida wa majiyar mu cewa aikin wanda shi ne wanda aka taba yi na farko a wannan yankin bai yi karko ba saboda dan kwangilar bai yi amfani da kayan aiki masu inganci ba.
 “Lokacin da ya zo, mun yi tunanin wannan aikin zai kawo mana karshen wahalarmu, amma abin takaici, bai dade ba ya daina aiki,cewar Malam Musa.
Ma’aikatar Ilimi ta Kano ta mayar da martani
 
 
 A zantawarsa da wakilin mu, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Lauratu Ado-Diso, ta tabbatar da cewa karamar hukumar Warawa na daya daga cikin kananan hukumomin da mafi yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Kano, inda ta kara da cewa gwamnati bata manta da karamar hukumar ba,akwai ayyuka gwamnati da suka ci gajiyar su a baya.
Tabbas garin Warawa na daya daga cikin kananan hukumomin Kano da ke da karancin ilimi da suka hada da barin makarantar sakandare da karancin shiga. Idan aka yi la’akari da haka, za aga cewa karamar hukumar za ta amfana da wasu ayyukan gwamnatin jihar. Kuma wasu daga cikin mazauna yankin an zabo su don cin gajiyar ayyukan Ci gaba na Commonwealth, FCDO.
 “An fara aiwatar da shirin ayyukan ne ta hanyar bada shawarwari ga Sarkin Gaya da kuma ganawa da manyan masu ruwa da tsaki a yankin na Warawa. Shirin ya dauki nauyin tallafawa koyarwa da koyo tun daga matakin farko don tabbatar da cewa duk wani bukatun makarantu  FCDO na tallafawa.
 “A karkashin Kwamitin Gudanarwa na Makarantu, shirin inganta SBMC, gwamnatin Jiha da ta Tarayya karkashin UBEC/SUBEB na hadin guiwar tallafin da suka bayar, sun raba tallafin makarantu ga unguwanni 5 domin su samu damar yin kananan gyare-gyare inda aka rabawa Garin Dau kudi mafi yawa kimanin ₦7m da kuma wani naira ₦2million ga Yandalla da wasu yankuna 3.
 Sakataren dindindin ya ce ba da tallafi ga al’ummomi mataki ne da ake bi daki -daki domin kuwa gwamnatin jihar ba za ta iya yin komai lokaci daya ba.
“Akwai muhimmin abu da muke yi don magance matsalar barin rashin zuwan yara makarantu, shine wayar da kan jama’a da wayar da kan iyaye da masu kula da su saboda su ma su yi abin da ake bukata da kuma tallafa wa gwamnati. Kamar yadda na fada a baya, Kanwa na daya daga cikin al’ummar Kano kuma akwai wasu ma kuma gwamnatin Kano na aiki kafada-da-kafada don magance wadannan matsalolin.”
 “MOE ta hada kai da hukumomin da suka dace kamar ma’aikatar raya al’umma da raya karkara wadanda aikinsu shi ne samar da irin wadannan ababen more rayuwa ga al’umma.yankunan da,ke da karancin kudade da bukatu marasa iyaka, gwamnati za ta samar da irin wadannan ayyuka a matakai,” in ji ta.
Wani kwararre kan ilimin boko a Sashen Ilimin Manya da Ayyukan Al’umma na Jami’ar Bayero Kano, Dokta Auwal Aliyu ya mayar da martani kan sakamakon wannan rahoto.
 Mista Aliyu ya ce yaran da ba sa zuwa makaranta na da matukar hadari ga tsaron kasa, inda ya ce al’ummomi irin su Kanwa da makwabtan su na iya fuskantar barazanar rashin tsaro matukar ba a yiwa lamarin tufkar hanci ba. Ya kara da cewa yin tafiya mai nisa na iya sanya yara musamman ‘ya’ya mata su fuskanci cin zarafi.
 “Yaran da ba sa makaranta, musamman ‘yan mata, ana samun sauƙin da kuma tasiri wurin shigar da su cikin munanan halaye. A wani bincike da kungiyar ‘ya’ya mata da ke kula da ilimin mata, wanda ni ma Mamba, babbar matsalar da muka gano shi ne, alkaluman kididdigar da aka samu na yaran da suka daina zuwa makarantun sakandire na faruwa ne saboda rashin samun tsaftataccen ruwan sha.”
Da yake kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kawo agaji ga al’ummomin da ke fama da matsalar ruwa irin su Kanwa, Mista Aliyu ya ce akwai bukatar a sake yin kwaskwarima ga tsarin samar da ruwan sha a jihar, tare da baiwa al’ummar karkara da ke fama da matsalar zuwa makaranta muhimmanci.
 “Dole ne gwamnati ta yi gaggawar sake tunanin samar da ruwa da kuma yadda za a samar da shi a fadin jihar. Ya kamata a mai da hankali ga wurare irin su Kanwa da sauran al’ummomi da rashin ruwa ke Yiwailla ga rayuwarsu musamman ta bangaren ilimi,” in ji shi.