Home Labarai Kar ku bari sai ranar rufewa sannan za ku karbi PVC ɗin ku — INEC

Kar ku bari sai ranar rufewa sannan za ku karbi PVC ɗin ku — INEC

0
Kar ku bari sai ranar rufewa sannan za ku karbi PVC ɗin ku — INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta shawarci masu rajistar zabe a babban birnin tarayya, FCT, da kada su jira sai ranar karshe kafin su zo karbar katin zabe na dindindin, PVC.

Shugabar sashen wayar da kan jama’a da wayar da kan jama’a, jinsi da kungiyoyin farar hula na INEC a babban birnin tarayya, Agnes Akpe ne ya ba da wannan shawarar a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a jiya Litinin a Abuja.

Akpe ta ce an fara karɓar katunan zabe a daukacin kananan hukumomi shida da ke FCT, kuma ana ba kowa shawara da ya je ya karbi katinsa a ofishin INEC da ke unguwar da yake zaune.

Ta ce a yayin da wadanda suka yi rajista a shekarar 2022 ko kuma suka nemi canja wuri su ka fara karbar nasu PVC din, an fara fara raba na tsoffin waɗanda su ka yi rijista.

“Ba zan ba kowa shawarar ya jira ba. Yanzu shine lokacin samun PVC. Zuwa da wuri ya fi muhimmanci,” in ji Mista Akpe.