
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta sake yin kira ga jam’iyyun siyasa da su dauki zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da za a yi ranar Asabar a matsayin takara ba yaki ba.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar ta INEC ne ya bayyana haka a wani taron kwamitin tuntuba tsakanin hukumomi kan harkokin tsaro, ICCES, a yau Talata a Abuja.
Yakubu ya bukaci shugabannin siyasa da su guji ayyukan da za su kawo cikas ga zaben ko kuma kawo cikas ga tsaron jami’an INEC da masu sa ido da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce za a gudanar da zaben gwamna a jihohi 28, ban da Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Ondo da kuma Osun inda aka gudanar da zaben ba tare da zagaye na biyu ba.
Ya kara da cewa za’a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a dukkanin mazabun jahohi 993 dake fadin kasar nan.