Home Labarai Kare ya cinyewa mai maganin gargajiya azzakari a Calabar

Kare ya cinyewa mai maganin gargajiya azzakari a Calabar

0
Kare ya cinyewa mai maganin gargajiya azzakari a Calabar

 

Wani mai maganin gargajiya, Ani Ikoneto ya rasa ransa bayan da karensa ya cire masa azzakari da ƴaƴan maraina ya kuma cinye su a ranar Kirsimeti.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, maƙwabtan Ikoneto, ɗan shekara 60 da yanke zaune a layin Jebbs da ke Calabar ta kudu sun baiyana cewa ya je ya shawu ne a ranar Kirsimeti inda ya dawo gida a buge.

Wani maƙwabcin mai maganin, mai suna Itoro, ya ce “mu mun riga mun kwanta amma wasu kuma sun ci gaba da hira a waje. Da ya dawo sai ya shiga dakinsa ya kwanta kuma bai rufe kofa ba. Da yana baccin, sai ya yi kashi.

“Shi kuma karen sai ya ji warin kashin sai ya sa karen ya shiga ɗakin nasa domin ya ci kashin. To da ya hau kan gadon, sai ya damƙi ƴaƴan marainan shi, ko ya zaci nama ne,” in ji Itoro.

Ya ƙara da cewa ihu da mai maganin ya yi ne ya ja hankalin mutanen da su ke zaune su na hira, inda su ka kai masa ɗauki su ka ga abin da ya faru.

“Mu na jin ihun sa sai mu ka zaci ko ƴan daba ne su ka kai masa hari, muna shiga sai mu ka duk jikin sa jini kuma da alamun gaban sa ya fice, sai mu ka shima karen duk bakin sa jini.

Itoro ya ƙara da cewa kafin su kai Ikoneto asibiti sai da su ka wawwanke masa jikin sa saboda kashi da jinin da ya ɓata shi.

Ya ce a lokacin da su ke gyara jikin nasa yana ta zubar da jini sosai inda kafin ma su karasa asibitin rai ya yi halinsa.

A washegarin Kirsimeti ne a ka kai shi ƙauyen su domin binnewa.