Home Labarai KAROTA ta kama matuƙin adaidaita-sahu bayan ya sace wa fasinja waya

KAROTA ta kama matuƙin adaidaita-sahu bayan ya sace wa fasinja waya

0
KAROTA ta kama matuƙin adaidaita-sahu bayan ya sace wa fasinja waya

 

Wani matuƙin babur mai ƙafa uku, wanda a Jihar Kano a ka fi sani da adaidaita-sahu, mai suna Abdullahi Baba-kura, ya shiga hannun jami’an Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, KAROTA bayan da ya sace wa fasinjansa wayar salula.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an cafke Baba-kura ne kwanaki biyu bayan kotu ta bada belin sa sakamakon aikata laifin ƙwace waya.

Dubun Baba-kura ta cika ne a jiya Litinin, bayan da ya ɗauki wani fasinja, su na tsaka da tafiya, sai ya yaudare shi ya kashe babur ɗin ya kuma ce fasinjar ya taimaka, garin taimakon ne ya zura hannu ya zare wayar.

Bayan fasinjan ya farga ne sai ya kama shi da kokawa, lamarin da ya ja hankalin jami’an KAROTA, inda bayan sun ji ba’asi, sai su ka damƙe shi a kan titin zuwa gidan gwamnati a garin Kano.

Da hukumar na tuhumar sa, Baba-kura da bakinsa ya amsa aikata laifin, inda ya ce kwanaki biyu kenan da bada belin sa a kotu.

Da ya ke jawabi a kan lamarin, kakakin KAROTA, Nabilusi Abubakar Ƙofar-Na’isa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce da zarar hukumar ta kammala bincike, za ta miƙa mai laifin ga rundunar ƴan sanda domin gurfanar da shi a kotu.