
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen hawa ta Jihar Kano, KAROTA ta sallami wani jami’inta bisa fasa wa wani direban adaidaitasahu gilashin babur a jihar.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa lamarin ya faru ne a titin IBB a birnin Kano a yau Laraba.
Jaridar nan ta gano cewa fasa gilashin babur ɗin ya haifar da ƴar hatsaniya daga al’ummar da ke gurin, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa a yankin.
Da ya ke bayani a kan lamarin, Kakakin hukumar ta KAROTA, Nablusi Abubakar Kofar-Na’isa, ya ce tuni hukumar ta tube kakin jami’in.
A cewar Kofar-Na’isa, tuni hukumar ta mika jami’in zuwa ga hannun ƴan sanda, inda ya ƙara da cewa jami’in ba maaikaci na dindindin ba ne.
Ya ƙara da cewa dama ma’aikatan Hukumar na wucin-gadi, idan su ka aikata irin wannan laifin, korar su ake yi sannan a hukunta su.
Ya kuma.ce KAROTA ba ta wasa da hakkin al’umma, inda ya ƙara da cewa duk wani jami’i da ya take hakkin farar hula to zai fuskanci fushin hukumar.