Home Labarai KARRAMAWA: Argentina ta sauya sunan filin attisayen tawagar ƙwallon ƙafar ta da sunan Messi

KARRAMAWA: Argentina ta sauya sunan filin attisayen tawagar ƙwallon ƙafar ta da sunan Messi

0
KARRAMAWA: Argentina ta sauya sunan filin attisayen tawagar ƙwallon ƙafar ta da sunan Messi

Argentina ta karrama kyaftin, Lionel Messi, bayan da ta sauya sunan wurin atisayenta da nashi.

Tun da fari, ana kiran wajen da Casa de Ezeiza, da ke Buenos Aires, wajen kwana da atisayen tawagar Argentina, inda yanzu zai ke amsa sunan Messi.

Hukumar kwallon kafar Argentina ce ta sanar da hakan, wadda ta ce wurin atisayen zai ke amsa sunan Lionel Andres Messi nan take.

Messi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022 kofi na uku da ta dauka jimilla a tarihi kenan.

Messi ya bi sawun Diego Maradona, wanda ya daukar wa Albiceleste kofin duniya a 1986.

”Wannan ce martaba mai girma da aka taba yi min a tarihi,” kamar yadda Messi ya sanar a kafarsa ta sada zumunta ta Instagram.

Ranar Alhamis Messi ya ci kwallo na 800 a tarihinsa na taka leda a karawar da Argentina ta doke Panama 2-0 a wasan sada zumunta.

Mai taka leda a Paris St Germain ya ci kwallo 99 a tawagar Argentina, wanda kofi daya ne kacal bai dauka ba a duniya shine French Cup.