Home Ilimi Kashi 90 na ɗaliban UNIMAID ba za su iya biyan ƙarin kuɗin makaranta ba — NAN

Kashi 90 na ɗaliban UNIMAID ba za su iya biyan ƙarin kuɗin makaranta ba — NAN

0
Kashi 90 na ɗaliban UNIMAID ba za su iya biyan ƙarin kuɗin makaranta ba — NAN

Kungiyar dalibai ta kasa, NANS, ta ce kashi 90 cikin 100 na daliban Jami’ar Maiduguri, UNIMAID, ba za su iya biyan kudaden makaranta da makarantar ta kara musu ba.

NANS ta bayyana haka ne a wani martani ga sabon matakin da magatakardar jami’ar, Ahmad Lawan ya bayyana cewa ɗaliban da ba za su iya biyan kudaden farar-daya ba za su iya biya kashi biyu.

Sai dai daliban a wata sanarwa da su ka fitar a jiya Alhamis mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar reshen jihar Borno, Mohammed Babagana, sun bukaci jami’ar ta yi musu bayani da kuma yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

“Wata sanarwar da hukumar UNIMAID ta fitar, inda ta bukaci dalibai da su biya sabon kudin makaranta da kuma cajin kudin a tsitstsinke, ya tabbatar da furucin da wasu dalibai suka yi cewa kudin ba kawai ya wuce kima ba, har ma da rashin mutuntaka idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu.

“Saboda haka, mu na kira ga daukacin daliban UNIMAID da kada su ci gaba da biyan ko wanne kudade, domin a halin yanzu shugabannin NANS na tattauna wa da hadin gwiwa kan lamarin.

“A kan haka, mu na kira ga babban ubanmu, Mataimakin Shugaban Jami’ar Maiduguri, wanda muka sani da ‘UBAN MARAYU na UNIMAID’ (mahaifin marayu) da ya taimaka wa dubban ‘ya’yansa wajen yin aikin ganin an koma baya. kudaden da sauran kudaden sun karu zuwa inda muke amfani da su,” in ji sanarwar.