
Hukumar Bunƙasa Magungunan Gargajiya ta Najeriya, NNMDA, ta ce har yanzu kashi 70 cikin 100 na ƴan Najeriya na amfani magungunan gargajiya, inda ta ce daɗaɗɗiyar al’ada ce tun da a ka halicci dan adam.
Dakta Samuel Etatuvie, Darakta-Janar na NNMDA, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Abuja, ya ce har yanzu al’adar amfani da magungunan gargajiya na nan daram.
Etatuvie ya ce wani bangare na aikinsu shi ne bincike, tattarawa, tattara bayanai kan kayayyakin ganye da su ka kasance na asali kuma sun riga sun yi bincike 14 daga cikin irin wadannan kayayyakin.
D-G ya kara da cewa biyar daga cikin ganyayyakin sun shiga jerin waɗanda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, ta tantance, yayin da sauran ke jira.
“Tun da aka halicci ɗan adam a ke amfani da maganin gargajiya, maganin gargajiya ya zo shekaru da yawa bayan magungunan asali wanda galibi ake yin shi a cikin yankunan karkara.
“A yau a Nijeriya da ma duniya baki daya, ana yin maganin gargajiya da na makarai a lokaci guda.
“A Nijeriya musamman, zan iya cewa muna da sama da kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya da ke hulɗa da masu maganin gargajiya da ke kula da lafiyarsu saboda yankunan karkararmu ba su da cibiyoyin kiwon lafiya na zamani.
“Game da magungunan ganye, muna da masu sana’ar magungunan ganyayyaki ko kayan lambu a kowace al’umma,” in ji shi.