
Rhoda Dia, Manajar Aikace-aikace ta shirin UNDP-GEF a kan samar da wadatar abinci mai taken IAP-FS, ta ce kusan kashi 97 cikin 100 na al’ummomin Nijeriya har yanzu su na amfani da itace wajen dafa abinci da sauran ayyuka.
Dia ta bayyana haka ne a yau Alhamis a wajen taron ƙara wa juna sani kan sanya amfani da dazuka da filaye a cikin dokar muhalli ta ƙasa, wanda ya gudana a Keffi, Jihar Nassarawa.
Ta ce sare bishiyoyi domin yin itacen ya lalata kasa tare da sanya wa ta fuskanci barazanar wasu matsaloli da za su sanya muhalli ya lalace da kuma matsalar samun wadatar abinci.
Ta ce akwai bukatar a samo bakin zaren warware wannan dabi’a ta wasu domin rage illar da sare itatuwa ke haifarwa wajen wadatar abinci a nan gaba.
Dia ta ce lamarin yana da ban tsoro, ta kara da cewa, “abin da muka gano daga rahoton mu shine kashi 97 na al’ummar mu na amfani da itace wajen girki.”
A cewarta, UNDP-GEF tana gudanar da ayyukan samar da dorewa da dauwama wajen samar da abinci wanda ake aiwatarwa a jihohi bakwai da suka hada da Kano, Katsina, Benue, Nasarawa, Gombe, Jigawa da Adamawa.
Ta ce ayyukan sun yi matukar tasiri wajen horar da mata da matasa kan samar da makamashi mai dorewa.