
Wata mata mai shekaru 68 mai suna Alhaja Iyabo, wacce aka ce ta yi asarar kudi sama da Naira miliyan 50 a rusau ɗin da ake yi a kasuwar Alaba Rago da ke Ojo da gwamnatin jihar Legas ta yi, ta rasu.
Iyabo mai sayar da shinkafa da wake ta samu bugun zuciya ne bayan ta gano cewa kudaden da ta samu a karshen mako ta ajiye a shagonta sun bace sakamakon rusau a safiyar Lahadin da ta gabata.
Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa a jihar a ranar 15 ga watan Mayu ta ba da sanarwar rusau ɗin ga ƴan kama-guri-zauna a cikin haramtattun gine-gine a kasuwar ta Alaba Rago, inda ta umurce su da su yi gaggawar tashi.
Shugabannin kasuwar da suke zantawa da manema labarai sun kiyasta cewa sun yi asarar da za ta kai Naira biliyan 50.
Sun ce buhunan shinkafa da wake da kuma dabbobi na daga cikin abubuwan da suka yi asara yayin rusau ɗin.
‘Yan kasuwa da dama da suka hada da Alhaja Iyabo sun ajiye cinikin da suka yi a karshen mako a cikin ma’ajiyar kasuwa, inda suke shirin kai kudaden a bankin ranar Litinin, amma sai mai afkuwa ta afku.