
Jirgin na farko na Qatar Airways ya sauka a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, MAKIA.
Jirgin ya sauka ne cikin farin ciki da ga masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jirgin, Boeing 787 Dreamliner, ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 11:10 na safe.
Jami’an hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama na tarayyar Najeriya FAAN ne su ka tarbe jirgin ta hanyar fesa masa ruwa kamar yadda a ka saba.
Jirgin na Qatar zai fara jigilar fasinjoji zuwa Kano a wani bangare na shirin fadada kasar.
Hakan zai biyo bayan Fatakwal, Jihar Ribas ranar Alhamis.
Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Jami’an Gwamnatin Jihar Kano da Kamfanin Jiragen Sama na Qatar Airways da dai sauransu sun tarbi Jirgin Qatar Airways zuwa Kano.