Home Siyasa Katin zaɓe 437,354 ne masu shi ba su karɓa ba a Osun

Katin zaɓe 437,354 ne masu shi ba su karɓa ba a Osun

0
Katin zaɓe 437,354 ne masu shi ba su karɓa ba a Osun

Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa a Jihar Osun, Dokta Mutiu Agboke, ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a a jihar da ba su karbi katin zabe na dindindin (PVC) ba da su je su karɓa a kan lokaci.

Agboke ya yi kiran ne a cocin Union Baptist Church, Odi-Olowo a Osogbo a jiya Lahadi, yayin da ya ke wayar da kan jama’a game da zaɓen 2023.

Ya ce, “Mutane da yawa sun ƙi karɓar PVCs dinsu. A Jihar Osun, mu na da PVC guda 437,354 da ba a karɓa ba. Wannan adadin na PVC ya isa ya zama an zaɓi gwamna da shi a jihar Osun.

“Ina so in yi kira gare ku cewa a kananan hukumominmu 30, za ku iya karbar katin zabe a can, mun kafe sunayen rajistar masu kada kuri’a a fadin jihar domin masu zabe su yi gyara a inda ake bukata,” in ji shi.