Home Labarai Kebbi: Yadda babban Limamin Sanchi da aka sace ya bayyana

Kebbi: Yadda babban Limamin Sanchi da aka sace ya bayyana

0
Kebbi: Yadda babban Limamin Sanchi da aka sace ya bayyana

Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘yan sanda jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an saki babban limamin garin Sanchi, Alhaji Maude Sanchi da wasu masu garkuwa da mutane suka sace.

Kamfanin dillanci Labarai ya rawaito cewa an sace Alhaji Maude ne a ranar 18 ga watan Maris.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Kabiru ne ya bayar da tabbacin sakin Alhaji Maude a yau Lahadi a yayin da ya ke yin wani jawabi ga manema labarai da aka kira don a sanar da su batun sakin na Alhaji Maude.

 “Babban limamin na cikin koshin lafiya kuma tuni ya koma cikin iyalinsa,” inji kwamishina ‘yan sanda.

Zuwa yanzu dai ‘yan sanda na ci gaba da binciken wadanda ke da hannu a cikin sace Alhaji Maude.

Ko a shekarar da ta gabata ma sai da wasu masu garkuwa da mutane suka sace Alhaji Maude, inda sai da aka biya su Naira miliyan 133 kafin su sake.

A wannan karin dai ‘yan sanda sun bayyana cewa masu garkuwar basu karbi ko sisin kobo ba kafin su saki Alhaji Maude.

Kwamishinan ‘yan sanda ya kara da cewa, jami’an ‘yan sandan jihar sun kama wasu mutum 3 a ranar 28 ga watan Maris dauke da bindigu kirar Hausa, kuma sashen bincike na rundunar na ci gaba da yin bincike akansu.