
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano, KEDCO ya baiwa yankunan da ya ke hulɗa da su haƙuri sakamakon ƙarancin wutar lantarki da a ke fuskanta a ƴan kwanakin nan.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kamfanin, Ibrahim Sani Shawai ya fitar, ya ce matsalar ta afku ne sakamakon raguwa da kason da a ke baiwa kamfanin da ga cibiyar raba wutar lantarki ta ƙasa.
A cewar Shawai, ita ma cibiyar raba wutar lantarkin ta fuskanci ƙarancin wutar ne sakamakon ƙarancin samar da wutar da ga Kamfanonin da su ke samar da wutar lantarki a ƙasar, waɗanda a ka fi sani da ‘Generation Companies’ zuwa ga KEDCO ɗin da ke baiwa Kano, Jigawa da Katsina wutar lantarki.
Ya ce an fi samun ƙarancin wutar da ga ƙarfe 6 na yamma da kuma 11 na dare.
Bayan da ya baiwa al’umma haƙuri, Shawai ya tabbatar da cewa za a shawo kan lamarin nan ba da daɗewa ba.