Home Labarai Ku riƙa tuƙin keke domin samun lafiyar jiki, FRSC ta shawarci ƴan Nijeriya

Ku riƙa tuƙin keke domin samun lafiyar jiki, FRSC ta shawarci ƴan Nijeriya

0
Ku riƙa tuƙin keke domin samun lafiyar jiki, FRSC ta shawarci ƴan Nijeriya

 

 

 

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta buƙaci ƴan Nijeriya da su ɗabbaƙa al’adar tuƙin keke domin samun lafiya da kuzari.

Kwamandan hukumar FRSC, reshen Jihar Kogi, Stephen Dawulung, ne ya bayar da wannan shawarar a cikin wata sanarwa da jami’in kula da wayar da kai na hukumar, Ayodeji Oluwadunsin, ya fitar bayan wani taro na shirye-shiryen zagayowar bikin ranar keke ta duniya na 2022 da ke tafe a ranar 3 ga watan Yuni.

“Tun shekaru da dama da su ka gabata, an tabbatar da cewa keke, abun hawa ne mai muhimmanci a cikin ababan hawa baya ga sauran fa’idodinsa na kiwon lafiya ga ɗan adam.

“Baya ga sanya birane su zama masu kyawun gani da tsafta, kamar yadda a ke gani a fili a biranen wasu ƙasashen Asiya, amfani da ababen hawa marasa injina kamar keken hawa na kawar da illar fitar da hayaƙin da ababen hawa ke fitarwa da gurɓata iska.

“Ta haka ne, hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, suka yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi keke domin inganta walwala tare da rage hadarurruka a hanyoyin Najeriya,” in ji Dawulung.

Kwamandan sashin ya ce bisa yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar za ta bullo da kuma hada shirye-shirye da ayyukan da za su haifar da hawan keke a matsayin ɗaya daga cikin ingantattun hanyoyin sufuri.

Ya yi nuni da cewa dogaro da motoci da aka yi ya sanya harkar sufurin a birane na Nijeriya ke fuskantar matsaloli idan aka yi la’akari da hauhawar farashin man fetur, inda hakan ke haifar da ƙarin amfani da man fetur da kuma cunkoso a hanyoyinmu.