Home Siyasa 2023: Na kere duk wani ɗan takara a cancantar zama shugaban ƙasa — Ngige

2023: Na kere duk wani ɗan takara a cancantar zama shugaban ƙasa — Ngige

0
2023: Na kere duk wani ɗan takara a cancantar zama shugaban ƙasa — Ngige

 

Ministan Ƙwadago da Samar da Ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa ba ma a jam’iyar APC ba kadai, hatta ‘yan jam’iyyar adawa sun san shi ya kere sauran masu son tsayawa takarar shugabancin kasar nan a cancanta.

Ofishin yada labarai na Ngige, a cikin wata sanarwa a yau Litinin ya ce Ngige ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa a Amansea, wani gari mai iyaka da jihar Enugu bayan ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

Sanarwar ta kara da cewa Ngige ya ba da bayaninsa na tuntubar jam’iyyun siyasa na adawa a lokacin da ya yi jawabi ga magoya bayansa a garin Amansea da ke kan iyaka da jihar Enugu bayan ya ziyarci Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi.

Ofishin yada labaran ya kuma bayyana cewa Ngige na da wannan yaƙini ne bayan da ya fahimci cewa har sauran jam’iyyu ma a na kaunar sa.

“Na ziyarci gwamnan jihar Enugu ne a wani bangare na tuntubar da nake yi a fadin kasar nan. Duk da cewa yana PDP, dan kabilar Igbo ne.

“Shi mutum ne mai gaskiya, mai kuma fahimta. Kar ku manta kuma Enugu ce babban birnin tsohon yankin Gabas. Kuma ka san cewa mu na mutunta juna ne.

“A cikin makon nan, na kuma tuntubi wasu ‘yan Najeriya da ba su da alaka da wata jam’iyyar siyasa. Don haka sai na tuntubi Gwamnan Jihar Enugu kan aniya ta tsayawa takara da kuma neman ra’ayinsa ma.

“Ya ce in harba kwallo a raga.

“Don haka wannan tafiya ba ta ‘yan APC kadai ba ce. ‘Yan uwanmu a PDP sun amince da cewa na fi wasu masu neman mukami a jam’iyyarsu,” in ji shi.