
Kungiyar ci gaban Gobir, wacce ke wakiltar dattawan al’ummar garin Gobir ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto da su samar da dukkan abin da ake bukata wajen tono gawar Sarkin Gobir da aka kashe.
‘Yan fashin daji ne dai suka kashe Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a yayin da suke tsare da shi a ranar 21 ga watan Agusta.
An yi garkuwa da Sarkin ne tare da dansa a hanyar su ta dawowa daga tattaunawa a fadar Sarkin Musulmai.
Daily Trust ra rawaito cewa da ya ke bayani ga manema labarai a Kano, mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Iliyasu Yusuf Gobir ya bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ake fuskanta da kuma gazawar gwamnati wajen magance matsalar.
“Al’ummar Hausawa, mussaman wadanda suke Gobir sun nuna hakuri a yayin da ake fusata su da kuma tada hankalinsu. Kodayake hakurin mu yazo karshe, mu na kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Sokoto da su dau kwakkwaran mataki wajen kawo karshen kashe-kashe da yin garkuwa da mutane”, inji Farfesa Gobir.
Ya kuma yi kira ga da a kara bunkasa tsaro a gabashin Sokoto da Sabon birni domin kare ‘yan kasa daga hare-hare.
” Al’ummar Gobir na neman gwamnatin tarayya da ta Sokoto su yi amfani da dukkan abinda suke da shi wajen dawo da gawar Sarkin Gobir don al’ummar sa suyi masa jana’iza cikin mutunci”.
Haka kuma, kungiyar ta soki fadar Sarkin Musulmai saboda kin yi musu gaisuwa na rashin da suka yi.