
Shugaban jam’iyyar APC, mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci mabiya addinin Kirista da su daina wata fargaba a kan tsayar da dantakarar shugaban kasa na 2023, Musulmi da mataimakinsa Musulmi da jam’iyyar ta yi.
Shugaban ya ce yanayin halin da siyasar kasar ke ciki ne a yanzu ya janyo hakan, wanda idan har jam’iyyar na son ta ci zaben 2023 sai ta yi hakan, amma ba abu ne da wani zai so ba a ce an yi wannan tsari.
BBC Hausa ta rawaito cewa Sanata Adamu ya ce zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin Sanata Bola Ahmed Tinubu, abu ne yin Allah.
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan wata ganawa ta sirri da Shugaban kasar Muhammadu Buhari, a Daura, Jihar Katsina a jiya Laraba, tsohon gwamnan na Nassarawa, ya ce bai kamata wannan zabi ya zama abin korafi ba ga al’ummar Kirista.
Ya ce: ”Gaskiyar lamari ita ce, ba abin da Allah Yake yi haka kawai. Allah Yana da dalilinsa na samar da manyan addinai biyu a kasar nan, kuma kowanne daga cikinsu, yana da mutanen da suke da dalilin binsa kuma suna hakki suma.”
”Akwai lokacin da Kirista ke jagorantar kasar nan. Yanzu kuma lokaci ne da Musulmi ke shugabantar kasar, ba za mu musanta wanna ba. Ba za mu iya samun lalle abin da muke so ba a wani lokaci, a ce dukkanin mu, mun amince da abu daya,” in ji shi.
Ya kuma kara da bayanin cewa, ” Ba lalle ba ne sai dukkaninmu mun kasance Musulmi ba ko kiristoci. Nufi ne na Allah a wannan lokacin cewa Shettima zai kasance mataimakin shugaban wannan babbar kasa, idan muka ci zabe. Abin da muke fata da kuma addu’a, wanda kuma muna kokarin cin zaben.”