
Shugabancin kungiyar ma’aikatan tashohi ta kasa, reshen jihar Kaduna, NURTW, ya ce matafiya a jihar sun ragu da sama da kashi 50 cikin 100 yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.
Bature Suleiyan, sakataren kungiyar NURTW a jihar ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kaduna.
Suleiman ya ce hakan ya faru ne saboda tsadar kudin sufuri, biyo bayan karin farashin man fetur.
“Mutane ba sa yin balaguro amma sun fi son aika saƙonni zuwa ga ƴan uwa da abokan arziki.
Abin takaici, idan ka je tashoshi a yanzu, za ka ga motoci da yawa suna jira ba tare da fasinjoji ba.
“Mutane ba su da kuɗin tafiya har sai ya zama dole, sun gwammace su aika saƙonnin waya,” in ji Mista Suleiman.
Ya ce masu motocin haya suna tafka asara saboda matsin tattalin arziki a kasar nan, ya kara da cewa, “Baya ga karin farashin man fetur, hanyoyi babu kyau da kuma tsare-tsaren da aka dauka kan harkar sufuri ba su da kyau. ”
Jami’in ya koka da yadda ake samun yan ƙungiyar da yawan karɓar haraji, wanda ya bayyana lamarin a matsayin mummunan abu.