
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano ta ce ta kama wani gungun masu ƙwacen waya su 6 da su ke addabar al’umma a jihar.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Ya ce an yi kamen ne bisa umarnin Sifeto-Janar na Ƴan Sanda kan cewa a tsaftace Kano daga duk wani aikin ɓatagari, musamman ƴan daba, ƴan ƙwaya da sauran laifuka, musamman a yayin bukukuwan Kirsimeti.
Kiyawa ya ce a na cikin sintirin ne a ka cafke waɗannan masu ƙwacen wayar su 6.
Ya ƙara da cewa an samu babura masu ƙafa uku da wayoyi 17 da su ka ƙwacewa mutane.
Kiyawa ya yi bayanin cewa masu laifin su na basaja ne a zuwan su matuƙa babur mai ƙafa uku ne sai su riƙa ƙwacewa fasinjoji wayoyin salula.
Ya ƙara da cewa idan an gama bincike, za ai kai su kotu domin su girbe abinda su ka shuka.