Home Kasuwanci KIRSIMETI: Za mu wadata ƴan ƙasa da man fetur — IPMAN

KIRSIMETI: Za mu wadata ƴan ƙasa da man fetur — IPMAN

0
KIRSIMETI: Za mu wadata ƴan ƙasa da man fetur — IPMAN

 

Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Ƙasa, IPMAN ta tabbatarwa ƴan ƙasa cewa za ta wadatar da man fetur a ƙasa yayin bukukuwan Kirsimeti.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Chinedu Okoronkwo ne ya bada tabbacin a yayin tattaunawa da Kamfanin Daillancin Labarai, NAN a ranar Laraba a Legas yayin da ya ke magana a kan dawowar layikan mai a gidajen mai.

Okoronkwo ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta hanzarta ta biya ƴan kasuwa biliyoyin nairori da su ke tsimaye daga gare ta.

“Mu na son mu nunawa ƴan ƙasa cewa a shirye mu ke mu haɗa kai da gwamnati domin wadata ƴan ƙasa da mai a yayin bukukuwan Kirsimeti da ma bayan Kirsimeti,” in ji Shugaban.