
Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ƴan Nijeriya cewa ba zai karya alƙawuran da ya ɗauka a mulkinsa ba.
Shugaban ya kuma tabbatar da ƙudurin gwamnatin sa na bunƙasa rayuwar al’ummar ƙasa.
Buhari ya baiyana hakan ne a saƙon shi na Kirsimeti ga ƴan ƙasa, wanda sashen yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa ya fitar a Abuja a yau Juma’a.
Shugaban ya kuma nuna baƙin cikin sa bisa aiyukan ɓatagari da ke haifar da rashin tsaro a ƙasa, wanda shugaban ya kira su da “mugaye a cikin mu,” inda ya ƙara da cewa ƙasar na fuskantar matsaloli duk da nasarorin da gwamnatin sa ta samu.
Ya ce “jajirtattun dakarun mu wanda mu ka ƙara musu ƙarfi da kayan aiki da kuma taimakon da su ke buƙata kullum cikin tunkarar waɗanan mugayen na cikin mu da su ke ƙoƙarin bata zaman lafiyar mu,”
Bayan ya zayyano irin aiyukan ci gaba da gwamnatin sa ta yi, Buhari ya ci alwashin bunƙasa rayuwar ƴan ƙasa baƙi ɗaya.