
Wata babbar kotun Kano ta sanya ranar 28 ga watan Yuli domin yanke hukunci a kan Abdulmalik Tanko, da ake tuhuma da laifin kashe wata yarinya ‘yar shekara biyar, Hanifa Abubakar.
Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar mai ɗauke da tuhume-tuhume biyar da suka haɗa da haɗin baki, yunƙurin yin garkuwa da mutane, haɗa kai s aikata laifin, garkuwa da mutane da kuma ɓoye gawa a kan Tanko, Hashimu Isyaku, mai shekaru 37, da Fatima Musa, mai shekaru 26, tun ran 14 ga watan Fabrairu.
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta laifukan da ake tuhumar su da su.
Mai shari’a Usman Na’abba, ya sanya ranar ne bayan da Lauyan da a ke ƙara da mai gabatar da ƙara suka kammala miƙa rubutattun bayanansu na ƙarshe.
Tun da farko, lauyan da ake ƙara, Hasiya Muhammad, a lokacin da ta amince da rubutaccen bayananta na karshe wanda ta miƙa wa kotu a ranar 31 ga watan Mayu, ta roki kotun da ta yi duba kan waɗanda ake kara tare da sallamar su.
Sai dai lauyan mai shigar da kara, mataimakiyar darakta mai shigar da kara na DPP, Rabi Ahmad, a cikin rubutaccen bayananta na ƙarshe, mai ɗauke da kwanan wata 6 ga watan Yuni ta kuma miƙa wa kotu a ranar, ta roki kotun da ta yanke wa wadanda ake tuhuma uku hukunci.
Ahmad ta bayyana cewa wanda ake kara na biyu (Isyaku) yana kan shari’a ne bisa laifin ɓoye gawa, laifin da ya saɓa wa tanadin sashe na 277 na kundin laifuffuka wanda kuma kuma ya cancanci hukuncin kisa a sashe na 274 (b).
A tuna cewa a na zargin Tanko, mamallakin makarantar Nobel Kids Comprehensive College, Kano, da yin garkuwa da Hanifa, a ranar 4 ga Disamba, 2021, inda ya yi garkuwa da ita a gidansa da ke Tudun Murtala na kwanaki kafin ya kashe ta kuma ya binne ta a ranar 10 ga Disamba. , 2021.
Laifin, ya saɓa wa tanadin sashe na 97, 95 da 273, 274(b) da 277 na kundin laifuffuka na jihar Kano na 1991.