Home Labarai Kisan nan da ake yi a Plateau ya isa haka, shugaban majalisar wakilai ya nuna ɓacin ransa

Kisan nan da ake yi a Plateau ya isa haka, shugaban majalisar wakilai ya nuna ɓacin ransa

0
Kisan nan da ake yi a Plateau ya isa haka, shugaban majalisar wakilai ya nuna ɓacin ransa

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa a Jihar Plateau, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama, yayin da wasu kuma suka rasa gidajensu.

Kakakin majalisar ya ce abin takaici ne idan aka karanta labarin sabbin hare-hare da tashin hankali a al’ummomin da ke kewayen karamar hukumar Mangu ta jihar.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Musa Abdullahi Krishi, ya fitar a jiya Alhamis, shugaban majalisar ya ce “ya isa haka” kan kashe-kashen da ake yi a Plateau.

Da yake cike da takaicin lamarin, Abbas ya ce zai gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan lamarin, yayin da majalisar za ta dauki matsaya mai karfi bayan dawowarta daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara a ranar Talata, mako mai zuwa.

Abbas ya kara da cewa, a ranar 30 ga watan Junairu, 2024, majalisar za ta fara shirye-shiryen shirya taron gangamin wayar da kai kan tsaro domin samar da dawwamammiyar mafita kan kalubalen tsaro a Arewa da sauran sassan kasar nan.