Home Labarai Kisan Sheikh Aisami: Buhari ya bada umarnin a bankaɗo ɓata-gari a sojoji

Kisan Sheikh Aisami: Buhari ya bada umarnin a bankaɗo ɓata-gari a sojoji

0
Kisan Sheikh Aisami: Buhari ya bada umarnin a bankaɗo ɓata-gari a sojoji

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin soji da su bankaɗo tare da kawar da duk wasu ɓata-gari a aikin soji da ke aikata muggan laifuka.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa a jiya Talata a Abuja ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu yayin da yake mayar da martani kan kisan gillar da aka yi wa wani malamin addinin Musulunci na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

Wani mugun soja ne ya kashe Sheikh Aisami kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.

Da yake mayar da martani kan lamarin a jiya Talata, Mista Buhari ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa malamin addinin Musuluncin ba tare da dalili ba, yana mai cewa:

“Wannan kisan gilla na wani mutum mai tausayi da wani soja da ya taimakawa ya yi ba shi da gurbi a horon sojoji.

“kisan ya kauce wa duk wata ɗabi’a ta rayuwar aikin soja wanda ya ginu a kan horo da mutunta tsarkakar rayukan ƴan ba ruwa na.

“Wannan lamarin na iya sanya al’umma su ji tsoron taimaka wa sojoji, ta yadda za su lalata alakar da ke tsakanin sojojinmu da fararen hula.”

Don haka shugaban ya yi kira ga hukumomin sojin kasar da su hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba tare da bata lokaci ba, tare da kawar da bankaɗo sauran ɓata-gari a cikin su masu irin wannan dabi’a.