
A yau Alhamis ne gwamnatin Kano ta sake gurfanar da da ɗan ƙasar China ɗin nan, Frank Geng-Quangrong, mai shekaru 47 a gaban Babbar Kotun Jiha bisa zargin kisan budurwarsa ƴar Nijeriya, Ummukulsum Sani, wacce a k fi sani da Ummita.
Ana tuhumar Frank, mazaunin anguwar Railway, da laifin kisan kai.
A ranar 4 ga watan Oktoba ne kotun ta umarci gwamnatin Kano da ta samo wa ɗan China ɗin tafinta.
Da aka sake gurfanar da shi a yau, lauyan gwamnati kuma babban antoni janar, Musa Abdullahi Lawan, ya gabatar da Guo Cumru, da ga ofishin jakadancin China domin ya yi wa wanda ake ƙara tafinta.
Ha shaida wa kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba a unguwar Janbulo, Ƙaramar Hukumar Gwale.
Mai gabatar da ƙarar ya zargi cewa a ranar ne da misalin ƙarfe 9 na dare ga caccaka wa Ummita wuka har ta rasu, bisa wani dalili da shi kadai ya sani.
“Mu yanzu a shirye mu ke, ba ma son mu bata lokaci sabo da tafintan a Abuja a ka dakko shi,” in ji Lawan.
Sai dai kuma wanda ake karar ya musanta zargin da a ke masa.
Kasan ha ce laifin da ake zargin ɗan China ɗin ya saɓa wa sashi na 221(b) na dokar laifuka ta Kano.
Alƙalin kotun, Sanusi Ado Ma’aji ya bayar da umarnin ajiye wanda a ke ƙarar a gidan yari.