
A yau Laraba ne a fara gabatar da shaidu a gaban kotu a shari’ar dan kasar Chinan nan, Geng Quangrong, wanda ake zargi da kashe matashiyar nan Ummukulsum Sani, wacce aka fi sani da Ummita, a gaban wata babbar kotu a jihar Kano.
Masu gabatar da kara su suka fara shiga da shaidunsu, inda a yau aka saurari mutum biyu, ciki har da mahaifiyar marigayiyar.
A zaman babbar kotun na yau, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya ci gaba da sauraren tuhumar da ake yi wa Mista da kashe tsohuwar budurwarsa Ummulkhuksum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita.
Hajiya Fatima Zubairu mahaifiyar Ummulkhuksum da kuma Asiya Sani, su ne shaidun, kuma sun yi wa kotu bayanin abin da suka sani game da zargin da ake yiwa Mista Geng.
Hajiya Fatima, ta faɗa wa kotun cewa a ranar 16 ga watan Satumbar 2022 Mista Geng Quangrong ya je gidansu inda ya yi ta buga kofa, bayan da suka bude kofar a cewarta, sai ya shiga dakin Ummita ya kulle kofar, da kuma ta leka ta taga sai ta ganta cikin jini, al’amakrin da yasa ta fita waje neman a kawo musu dauki.
Barista Muhammad Balarabe Dan Azumi shi ne lauyan Mista Geng, ya kuma yi wa Hajiya Fatima da Asiya Sani tambayoyi a gaban kotun.
Lauya mai gabatar da kara kuma kwamishinan Shari’a na jihar Kano Musa Abdullahi-Lawan shi ya jagoranci lauyoyin gwamnati a zaman kotun.
An shafe sa’o’i ana zaman saboda musayar bayanai da tambayoyi da aka riƙa yi wadanda suka dauki hankali sosai, abin da yasa har hutu aka ta fi har sau biyu.
Alkalin babbar kotun Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage zaman zuwa gobe da kuma jibi juma’a inda ake fatan ci gaba da sauraren shaidu.