
Hukumar Lura da Harkokin Sadarwa, NCC, ta tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa adadin masu amfani da yanar gizo a kasar sun kai miliyan 98.3 a watan Disambar 2017.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo, inda ta ke fadin adadin mutanen da ke aiki fa yanar gizo a Nijeriya a kowane wata, inda a yau Alhamis ta fitar da masu amfani da yanar gizo na watan Disambar bara.
Jadawalin ya nuna cewa layikan Airtel, MTN da Glo sun fi yawan mabiya masu amfani da tsarin data dinsu, a yayin da 9mobile ke da karancin mabiya.
A watan Nuwamba, jadawalin ya nuna cewa masu amfani da yanar gizo da yawansu ya kai:94, 818,553. Inda a watan Disamban 2017 din dai, adadin ya kai: 98,391,456. Hakan na nuna cewa a tsakanin Nuwamba zuwa karshen Disamba 2017 an samu karin mutane miliyan 3, 572,903.
Masu amfani da datar MTN ne suka fi karuwa a tsakanin Nuwamba zuwa Disamba. MTN ta samu adadin sababbin mutane 2,642.666. Hakan ya daga yawan masu amfani da yanar gizon MTN daga: 33,426,931 zuwa 36,069,597.
9mobile kuma raguwa ta samu, inda masu amfani da datarta har mutum 68,341 suka canza sheka suka koma wasu layikan. Wannan ya rage adadin masu amfani da datar 9mobile daga 1,407,180 a watan Nuwamba zuwa 1,338.839.
Airtel ta samu karin sababbin masu amfani da datar ta da yawansu ya kai 911,040 a watan Disamba, wanda ya daga yawan masu amfani da datar Airtel zuwa 23,985,203 a Disamba daga 23,074,163 da suke da su a Nuwamban 2017.
Suma Globacom sun samu karuwar sababbin mutane da yawansu ya kai 87,538. Hakan ya daga adadin masu amfani da datarsu zuwa 26,997,817 a watan Disamba daga 26,910,279 da suke da su a watan Nuwamba.