
Daga Buhari Abba
Aikin jarida aiki ne na ƙwaƙwalowa, bincikowa tare da gabatar wa jama’a sabon labari ko yaushe. Aiki ne da ya ke buƙatar Ilimi, jajircewa, sadaukarwa da kuma rashin son abin duniya da tsoron fadar gaskiya a bakin aiki. Kuma duk wanda ya ke son zama cikakken Dan Jarida kuma gangaran a Wannan fagen to babu shakka lalle zai zama mai ƙwaƙwar sanin komai, musamman abin da ya shafi rayuwar al’umma
La’akari da irin gudummawa da rawar da yan jaridu ke takawa a al’amuran yau da kullum na rayuwar al’umma, wadanda su ka hada da Ilimantarwa, Wayarwa, Fadakarwa da kuma Nishadantarwa ya sanya dan jarida ya zama shi ne Fitilar al’umma
Kamar yadda mu ka Sani jihar Kano jiha ce da ta zama cibiyar siyasa kasar nan, wannan ya sanya ta kasance daya daga cikin jihohin da su ke da kafafen yada labarai masu zaman kan su birjik a fadin jihar. Kuma a kullum Idan ka kunna daya daga cikin tashoshin radiyon, to tabbas za ka ji amon masu rajin kare hakkin bil’adama da kuma yaki da cin hanci da rashawa
Katsam ana tsaka da aikin yaki da cin hanci da rashawa a Fadin kasar nan ta hanyar kafafen yada labarai, Kungiyoyin fararen hula da kuma Kungiyoyin mata, sai faduwa ta zo dai-dai da zama domin wani fitaccen Dan jarida kuma gangaran a wannan fannin ya zakulo wani Babban al’amari mai alaka da cin hanci da rashawa, cikin wani Faifan bidiyo da aka hasko fuskar Gwamna Jihar Kano yana karbar kudin kasar Amurka wato Dala a hannun yan kwangila
Masana da masu sharhi akan Al’amuran yau da kullum sun yi sharhi akan wannan batu, yan takarda da malaman Jami’a suma sun tofa albarkacin bakin su.
Kawo yanzu dai kallo ya koma sama, domin al’ummar kasar nan sun zuba ido wajen ganin yadda wannan kura da Jaafar Jaafar ya tayar za ta karge! Domin kuwa ko a cikin wannan shekarar ya wallafa wani rahoto akan mai martaba Sarkin Kano Mal Muhammad Sunusi II, wanda daga karshe rahoton ya yi awon gaba da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano
Abin tambayar a nan shi ne ko wannan wallafa da Jaafar Jaafar ya yi za ta bude wani sabon babi ga gidajen radiyo masu zaman kan su akan yaki da cin hanci da rashawa a jihar Kano da ma kasa baki daya, ta hanyar yin binciken kwakwaf tare da hada rahoto? (Duk da cewa akwai wani gidan Radiyo guda daya da ya yi suna tare da yin fice wajen dakile harkar rashawa da cin hanci)
Wanne tasiri ko kaimi hakan zai baiwa matasan yan jaridu da ke tasowa? Domin kuwa masana a Wannan harkar sun dade da ganin cewa da yawa daga cikin matasan yan Jarida sun zama yan abi yarima a sha kida ko kuma zama karnukan farautar yan siyasa