Home Siyasa Na koma jam’iyyar ADP ne sabo da bata yi wa kowa laifi ba a Kano — Shaaban Sharada

Na koma jam’iyyar ADP ne sabo da bata yi wa kowa laifi ba a Kano — Shaaban Sharada

0
Na koma jam’iyyar ADP ne sabo da bata yi wa kowa laifi ba a Kano — Shaaban Sharada

 

 

 

Tsohon hadimin Shugaban Ƙasa, Sha’aban Sharada ya ƙaddamar da takararsa ta gwamna a jam’iyyar ADP
Sha’aban Sharada ya ƙaddamar da takararsa ta gwamna a jam’iyyar ADP
09/03/2022 Muhsin Gambo Dauda

Ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar ADP mai alamar littafi, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya ce ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa jam’iyar ne sabo da bata yi wa kowa laifi ba a jihar.

Sharada ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke ƙaddamar da takararsa a hukumance a yau Asabar, a Sani Abacha Youth Centre a Kano.

Haka kuma ya ƙara da cewa, matuƙar ya kafa gwamnati a jihar Kano zai tabbatar da cewa, dukkan asibitocin jihar Kano sun samu wadatattu kuma ingantattun kayayyakin aikin lafiya.

A cewar sa, idan ya kafa gwamnati a Kano, zai samar da asibitoci na zamani a ɗaukacin mazaɓu 484 a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Sha’aban ya ƙara da cewa “Idan na kafa gwamnati zan tabbatar da cewa ƙananan hukumomi sun samu cikakken ƴancin cin gashin kai”.

Ya kuma yi alkawarin baiwa ƙananan hukumomi cin gashin kansu domin su ci gaba da yi wa al’umma ayyukan ci gaba don magance talauci.

Ya kuma kara da cewa a Kano babu wata jam’iyya mai farin jinin ADP, inda ya ce idan ta ci zaɓe to za ta saka wa al’umma da irin goyon bayan da su ke ba ta.