Home Labarai Komai girman ka indai ka shigo jam’iyyar APC to ni kakan ka ne — Ganduje

Komai girman ka indai ka shigo jam’iyyar APC to ni kakan ka ne — Ganduje

0
Komai girman ka indai ka shigo jam’iyyar APC to ni kakan ka ne  — Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shi kakan duk wani dan jam’iyyar APC ne, sabo ko tsoho, kuma yanzu a karkashin sa yake saboda shi ne shugabanta na kasa.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da shugabannin kungiyoyin jam’iyyar APC a jiya Juma’a a Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Alhamis ne Ganduje, tsohon gwamnan Kano, ya roƙi gwamnan mai-ci, Abba Kabir Yusuf da ya dawo jam’iyyar APC.

Sai dai kuma da ya ke jawabi a wajen taron na jiya, Ganduje ya yi wani jirwaye da kamar wanka, inda ya nuna cewa ko da gwamna Abba ya shigo APC, to fa a ƙarƙashin shugabancin sa (Ganduje) zai zauna

” Menene aikin shugaban jam’iyyar APC na kasa ? Aikine na jam’iyya a jihar Kano kawai ? Jihohi 36 da Abuja duk inda naje nine yallabai nine alasabbanani, nine Sheikh, duk inda naje nine alangoburo, saboda haka na zaga kasar nan ina kiran gwamnoni su shigo jam’iyyar APC don mu samu karuwa, to meye laifi idan na yi haka a jihata ta kano?, in ji Ganduje

Shugaban jam’iyyar na ƙasa ya ce ya sami nasarar shigo da ƴan kananan jam’iyyu, ciki har da NNPP a jihar Bauchi, “don haka a kano ma, Ina rokon yan Jam’iyyar NNPP mai kayan gwari da su yi maza kada kayan gwari su rube, su zo inda za a adana musu su a firji don kada su lalace”.

” Yanzu laifi ne dan na kirawo yan Jam’iyyar NNPP na jihar Kano su dawo APC?, ai wanda yake da shi, shi ake roko, wanda yake da shi shi ya ke bayarwa.

” Kada ka ji tsoro idan wani ya zo cin arziki a gidanka, shin da ka je kaci arziki a gidanka shi da ya zo yaci arziki a gidanka wanne ka fi so? , Ai mai shi shi yake da abun bayarwa, marashi shi ne mai neman wurin shiga”.

“Saboda haka, mu na rokon su su auna cewa shugabancin kasar nan a jam’iyyar NNPP zai samu?, to sabo da haka kiran su su dawo jam’iyyar APC ai abun alfahari ne mu a wajen mu. Don haka mu kari muke nema, kuma kamar yadda na fada muku indai ka shigo jam’iyyar ko kai jagorane to nine shugabanka”.