Home Siyasa Koodinetan takarar Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa PDP in Bauchi

Koodinetan takarar Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa PDP in Bauchi

0
Koodinetan takarar Kwankwaso ya fice daga NNPP zuwa PDP in Bauchi

Dr Babayo Liman, kodinetan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP a jihar Bauchi.

Liman, wanda shi ne Sakataren Jam’iyyar na shiyyar Arewa-maso-Gabas ya sanar da murabus dinsa a wani taron manema labarai a jiya Litinin a Bauchi.

“Ina so in sanar da jama’a musamman ‘yan jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi da Arewa maso Gabas da Najeriya baki daya cewa na yi murabus daga matsayina na dan jam’iyyar NNPP.

“Na kuma yi murabus daga matsayina na Sakatare na shiyyar Arewa maso Gabas da kuma mamba kuma kodineta na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabiu Kwankwaso.

“Bari jama’a su sani cewa na janye daga jam’iyyar NNPP, Ni ba dan jam’iyyar NNPP daga yau,” inji shi.

Ya ce ya fice daga NNPP zuwa PDP tare da dimbin magoya bayansa, inda ya ce jam’iyyar ba ta da tsarin da za ta iya lashe zabe a kasar nan.