
An kori Ministar Jinsi ta Ghana, Sarah Adwoa Safo da ga aiki, bayan da rahotanni su ka bayyana cewa ta shafe fiye da shekara ba tare da ta je aiki ba.
Fadar gwamnatin ƙasar ba ta bayyana dalilin da ya sa aka kore ta ba a sanarwar da ta fitar, amma akwai yiwuwar saboda daɗewar da ta yi ne ba ta zuwa aiki.
Sai dai kuma BBC ta rswaito cewa tuni aka naɗa ministan riƙon ƙwarya a ma’aikatar.
A baya, Sarah ta nemi izinin hutu daga Shugaban Ƙasa Nana Akufo-Addo wanda ya ƙare tun a watan Agustan shekarar da ta gabata kuma aka tsawaita mata wa’adinsa.
Kazalika, matar ta ƙaurace wa majalisar dokokin ƙasar a matsayinta na mai wakiltar Dome Kwabenya da ke Accra babban birnin ƙasar.
Ana sa ran nan gaba kaɗan Kakakin Majalisa Alban Bagbin zai gabatar da rubutaccen ƙudiri da zai kai ga ayyana kujerarta a matsayin fanko.