Home Lafiya Korona: Har yanzu Omicron ba ta kashe kowa a Nijeriya ba — NCDC

Korona: Har yanzu Omicron ba ta kashe kowa a Nijeriya ba — NCDC

0
Korona: Har yanzu Omicron ba ta kashe kowa a Nijeriya ba — NCDC

 

Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta ce babu wani mutum da ya rasa ransa da ga ɓullar sabon nau’in korona mai suna Omicron.

Darakta-Janar na NCDC Ifedayo Adetifa ne ya baiyana hakan ga manema labarai a Abuja a yau Juma’a.

Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa ƙididdiga da ga Taraiyar Afrika ta nuna cewa sabon nau’in na korona na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar daji a Afirka.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Taraiyar Afirka ɗin ta ce ƙasashe 22 ne su ka bada rahoton ɓullar cutar ta Omicron.

Da ya ke ci gaba da jawabi, Adetifa ya ce Omicron ta ninka yawan mutanen da a ke samu da cutar korona har sau 500, inda ya ƙara da cewa yanzu ta kasance nau’in korona da ya fi yaɗuwa a ƙasar.

Shugaban na NCDC ya baiyana cewa an ƙara samun mutum 45 ɗauke da cutar inda hakan ya kai adadin zuwa 51.

Ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi riƙo da matakan kariya da ga kamuwa da cutar.