Home Lafiya Korona ta kashe sama da mutane dubu 3 a Nijeriya — NSCDC

Korona ta kashe sama da mutane dubu 3 a Nijeriya — NSCDC

0
Korona ta kashe sama da mutane dubu 3 a Nijeriya — NSCDC

 

A cewar hukumar ta NCDC, sabbin mutum 859 suka kamu da cutar a ranar Litinin da ta gabata.WASHINGTON D.C. —

Hukumar da ke Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa, NCDC ta ce mutane 3, 024 cutar korona ta kashe tun daga lokacin da annobar ta ɓarke zuwa yanzu.

NCDC ta bayyana hakan ne a ƙididdigar da ta fitar a jiya Litinin, wacce ta baiyana iya adadin sabbin kamuwa da cutar.

A cewar hukumar, mutane 859 ne su ka sake kamuwa da cutar da ga jiya Litinin.

Daga cikin wannan adadi, in ji NCDC, mutane 555 a jihar Legas a ka same su, 57 a babban birnin tarayya na Abuja sai jihar Rivers mai mutane 44.

Sauran jihohin sun haɗa da Filato mai mutum 43, Edo mutum ɗaya da Ondo mai mutane 34.

Kwara na da mutane 23, Kano 18, Ogun 16, Enugu 11, Oyo 6, Delta 5, Bauchi 3 sai Bayelsa mai mutum 3 ita ma.

Hukumar ta NCDC ta ce jimullar mutanen da a ka gano cutar ta harba a ƙasar baki ɗaya ta tsaya a dubu 238, 420 ya zuwa ranar Litinin.