Home Lafiya Korona na nan na ƙara bazuwa, in ji WHO

Korona na nan na ƙara bazuwa, in ji WHO

0
Korona na nan na ƙara bazuwa, in ji WHO

 

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi gargaɗin cewa jerin waɗanda suka kamu da cutar korona na nuna cewa har yanzu ba a kuɓuta daga annobar ba.

TedrosAdhanom Ghebreyesus ya ce cutar na ci gaba da yaɗuwa, don haka akwai buƙatar ƙasashe su ɗauki matakan ɗakile ta.

Ya ce, ya damu da yadda ake samun ƙaruwar kamuwa da cutar korona.

Wannan lamari yana ƙara takura tsarin kiwon lafiya dake cikin matsi, da ma su ma’aikatan lafiyar.

Yana jawabi ne a wajen taron kwamitin na WHO, wanda ya yanke hukuncin cewa har yanzu annobar na da haɗari ga lafiyar al’umma.

Kwamitin ya bayyana damuwa cewar an samu raguwar yin gwajin cutar a duk faɗin duniya, wanda hakan kuma ya shafi yadda ake sa ido a kan yaɗuwarta.